Tsohon Shugaban Kasar Cuba Fidel Castro Ya Rasu
https://parstoday.ir/ha/news/world-i14413-tsohon_shugaban_kasar_cuba_fidel_castro_ya_rasu
Gwanatin kasar Cuba ta sanar da rasuwar tsohon shugaban kasar Fidel Castro, bayan kwashe tsawon shekaru yana jinya tsai-tsaye.
(last modified 2018-08-22T06:59:18+00:00 )
Nov 26, 2016 03:26 UTC
  • Tsohon Shugaban Kasar Cuba Fidel Castro Ya Rasu

Gwanatin kasar Cuba ta sanar da rasuwar tsohon shugaban kasar Fidel Castro, bayan kwashe tsawon shekaru yana jinya tsai-tsaye.

Shugaban kasar ta Cuba Raul Castro dan uwa ga marigayi Fidel Castro ne ya  sanar da hakan dazu ba da jimawa ba, inda ya ce za a sanar da shirye-shiryen da za a yi a daga bisani.

Fidel Castro dan shekaru 90 a duniya, shi ne ya jagoranc juyin juya halin gurguzu a kasar Cuba, wanda ya kawo karshen mulkin jari hujja da Amurka ke mara wa baya  akasar ta Cuba a shekara ta 1959.