Julian Assange: CIA Da Saudiyya Ne Suka Kirkiri Da'esh (ISIS)
Mutumin nan da ya kirkiro shafin kwarmaton nan na Wikileaks Julian Assange ya bayyana cewar Amurka da Saudiyya su ne tushen da suka kirkiro kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh (ISIS).
A cikin wani rahoto da ta watsa, Tashar talabijin din Press TV, ta bayyana cewar Julian Assange ya bayyana hakan ne a lokacin da yake shirin sake fitar da wasu sabbin bayanai rabin miliyan a jiya Litinin inda yayi karin bayani dangane da abubuwa da kuma matakan da aka bi wajen yaduwar ta'addancin a yankin Gabas ta tsakiya.
Mr. Assange ya zargin hukumar leken asirin Amurka CIA da kuma gwamnatin Saudiyya a matsayin wadanda suka share fagen haihuwa da kuma yaduwar kungiyoyin 'yan ta'addan a yankin Gabas ta tsakiyan yana mai ishara da irin biliyoyin dalolin da hukumar ta CIA da kuma gwamnatin Saudiyya suka ware wajen sayen makamai wa kungiyoyi masu dauke da makami a kasar Afghanistan da nufin yakar tsohuwar Tarayyar Sobiyeti a matsayin matakin farko na yaduwar ayyukan ta'adancin.
Mr. Assange ya kara da bulla kungiyar Al-Qa'ida da kuma kai harin 11 ga watan Satumba shi ya share fage wa Amurka na mamaye Afghanistan da Iraki kana daga baya kuma suka share fagen shigowa da munanan akidar tsauin ra'ayi wanda ya haifar da kungiyar ta'addanci nan ta ISIS bisa goyon baya da kuma dukiyar su.
A baya ma dai tsohuwar sakatariyar wajen Amurka Hilary Clinton ta yi wannan ikirarin na cewa Amurka ce ta samar da kungiyar ta ISIS lamarin da ke tabbatar da ikirarin da ake yi na hannun Amurka da Saudiyyan cikin samar da wanann kungiya.