A Yau Ministan Tsaron Faransa Zai Ziyarci Kasar Chadi
Sabon ministan tsaron kasar Faransa zai fara gudanar da ziyara ta farko a wajen kasar Faransa zuwa kasar Chadi a yau, domin ganawa da dakarun Faransa da ke sansaninsu a birnin Njamina, da kuma jami'an gwamnatin kasar ta Chadi.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya habarta cewa, ziyarar ministan tsaron kasar Faransa Berner Kaznov zuwa kasar Chadi a yau, na da nufin kara karfafa gwiwar sojojin kasar ne wajen ci gaba da gudanar da aikinsu a cikin kasashen yankin Sahel, wato Chadi, Nijar, Mali, Burkina Faso da kuma Mauritaniya.
Kamar yadda kuma zai gana da shugaba Idris Deby da wasu manyan jami'ai na kasar, da kara jaddada goyon bayan gwamnatin Faransa ga gwamnatin Idris Deby wajen yaki da ayyukan ta'addanci.
Faransa na da sojoji da suka kai kusan 4000 a Chadi, amma wasusunsu suna gudanar da ayyukansu ne a wasu kasashen yankin Sahel, domin yaki da kungiyoyin da ke da'awar jihadi.