Syria : Hollande, Ya Bukaci A Mutunta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta
https://parstoday.ir/ha/news/world-i16129-syria_hollande_ya_bukaci_a_mutunta_yarjejeniyar_tsagaita_wuta
Shugaban kasar Faransa, François Hollande ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki kan rikicin Syria da su mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.
(last modified 2018-08-22T06:59:29+00:00 )
Jan 05, 2017 08:26 UTC
  • Syria : Hollande, Ya Bukaci A Mutunta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta

Shugaban kasar Faransa, François Hollande ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki kan rikicin Syria da su mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.

hakan dai a cewar Mista Hollande zai bada dama mai kyawo ta kaiwa ga tattaunawar zamen lafiya da za'ayi kan rikicin kasar a watan Fabariru mai zuwa a Geneva.

Mista Holande ya kara da cewa ya kamata bangarorin su dukufa kan duk abunda zai samar da ci gaba domin kaiwa ga wannan tattaunawar kamar yadda MDD ta tsara.

A watan Fabariru mai zuwa ne aka shirya yin tattaunawar ta masu ruwa da tsaki kan rikicin kasar ta Syria, aman kafin nan za'ayi wata ganawa a shiga tsakanin kasashen Rasha da Iran da kuma Turkiyya a karshen wannan watan da muke ciki.