Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi Ta Jaddada Muhimmancin Yaki Da Ta'addanci
Babban daraktan bangaren kula da harkar ilimi da al'adu na kungiyar hadin kan kasashen musulmi "ASESCO" a takaice ya bayyana cewa: Yaki da ta'addanci yana bukatar hadin gwiwa tsakanin dukkanin kungiyoyin kasa da kasa.
A jawabinsa a zaman taron kasa da kasa kan rawar da kafofin watsa labaran kasashen Larabawa zasu taka a fagen yaki da ta'addanci da aka gudanar a kasar Masar: Abdul Aziz bin Usman Altuwijari ya bayyana cewa; Yaki da ta'addanci lamari ne da ke bukatar hadin kan dukkanin kungiyoyin kasa da kasa da gwamnatocin kasashe da kuma cibiyoyi da kungiyoyi masu zaman kansu na addinai da fararen hula gami da kafofin watsa labaran duniya.
Binu Usman ya kara da jaddada cewa; Ayyukan ta'addancin da ake gudanar a duk fadin duniya ba su da wata alaka da koyarwar addinin Musulunci ko al'ummar musulmi saboda kungiyoyin 'yan ta'adda na duniya suna da wasu manufofi ne tasu ta kansu da suke son cimmawa.