Amurka Ta Janye Wani Bangare Na Takunkuminta A Kan Sudan
Gwamnatin kasar Amurka ta janye wani bangare na takunkuman da ta kakaba wa kasar Sudan, amma har yanzu tana cikin jerin kasashen da Amurka ke kira masu danne hakkokin bil adama.
Shugaban kwamitin kula da siyasar wajen Amurka a majalisar dokokin kasar Edd Ruis ya bayyana cewa, matakin da shugaba Obama ya dauka a jiya na janye wani bangaren takunkumin Amurka daga kan kasar Sudan abu ne mai kyau, amma kuma hakan ba ya nufin cewa Sudan ta fita daga kasashe masu keta hakkokin 'yan adam.
Tun kafin wannan lokacin dai gwamnatin Sudan ta roki Amurka da ta janye takunkuman da ta kakaba mata, bayan da Sudan din ta amince da wasu sharudda da kaidoji da Amurka ta gindaya mata, duk kuwa da cewa har yanzu sammacin da kotun manyan laifuka ta duniya ta bayar da shugaban kasar Uamr Hassan Albashir na nan daram.