(EU) Ta Bukaci Trump Ya Mutunta Yarjejeniyar Nukiliyar Iran
(last modified Wed, 18 Jan 2017 06:25:22 GMT )
Jan 18, 2017 06:25 UTC
  • A watan Yuli 2015 ne aka cimma yarjejeniyar da Iran
    A watan Yuli 2015 ne aka cimma yarjejeniyar da Iran

Kungiyar Tarraya Turai ta bukaci bangaren zababen shugaban kasar Amurka Donald Trump daya mutunta yarjejeniyar nukiliyar da kasashen duniya suka cimma da kasar Iran.

Kungitar ta EU ta ce ta tuntubi bangaren na Donald Trump ta bayan fage, kan batun yarjejeniyar da aka cimma da Iran inda ta ce yana da kyawo a mutuntunta yarjejeniyar mai cike da mahimanci.

Babbar jami'ar diflomatsiya kungiyar kasashen Turan Federica Mogherini ta kara nanatawa a ranar Litinin cewa kasashen Turan na mutunta yarjejeniyar, kum a yanzu haka tana aiki kafada da kafada da kasashen Rasha da Sin bisa wannan batu.

Zababen shugaban kasar Amurka dai Donald Trump dai a cikin yakin neman zabensa ya sha sukan yarjejeniyar da kasashen da suka hada da Amurka, Sin, Rasha, Jamus, Faransa da kuma Biritaniya suka cimma da Iran a watan Yuli na shakara 2015.

Yarjejeniyar dai ta tanadi dagewa Iran takunkumin da aka kakaba mata a yayin da ita kuwa zata sassauta shirin nukiliyarta na zamen lafiya.