Muftin Kasar Masar Ya Jaddada Wajabcin Yaki Da Ta'addanci
Muftin kasar Masar ya jaddada wajabcin samun hadin kan kasashen duniya a fagen yaki da ayyukan ta'addanci.
A ganawarsa da jakadan kasar Australiya Neil Hawkins a birnin Alkahira a yau Alhamis: Muftin kasar Masar Shawki Ibrahim Abdul-Karim Allam ya bayyana cewa: Ta'addanci da tsaurin ra'ayin addini na wuce gona da iri suna matsayin manyan barazana ga zaman lafiyan duniya, kuma babu wata kasa da ta kubuta daga wadannan masifu, sakamakon haka hanya daya tilo ta kawo karshen wadannan masifu ita ce samun hadin kan kasashen duniya a fagen murkushe su daga kan doron kasa.
Shawki Ibrahim ya kara da jaddada cewa: Ayyukan ta'addanci da tsaurin ra'ayin addini na wuce gona da iri ba su da wata alaka da addinin Musulunci saboda addinin Islama da dukkanin addinan da suka zo daga Allah suna watsa akidar soyayya da 'yan uwantaka ne a tsakanin jinsin bil-Adama.
A nashi bangaren jakadan kasar Australiya a kasar ta Masar Neil Hawkins ya bukaci bangaren da ke kula da fitar da fatawowi na addinin Islama a Masar da ya kara matsa kaimi a fagen yaki da ta'addanci da tsaurin ra'ayin addini.