Mexico Ta Mika Madugun Masu Safarar Kwaya El-Chapo Ga Amurka
Gwamnatin kasar Mexico ta mika wa Amurka kasurgumin shugaban masu fataucin miyagun kwayoyi dan kasar Joaquin Guzman da ake kira El Chapo domin fuskantar shari’a kan tuhumce-tuhumcen da ake masa a kasar Amurkan.
Gidan talabijin din kasar Mexicon ya nuna hoton lokacin da aka dauko Mr. Guzman El-Chapo din a daure daga gidan yarin da ake tsare da shi inda aka sanya shi cikin wani karamin jirgin sama kafin aka tafi da shi inda aka mika shi ga mahukutan Amurkan.
Wasu rahotanni sun ce a wani lokaci a yau din nan Juma'a ne mahukuta a Amurkan za su gurfanar da shi a gaban wata kotu a birnin New York don gabatar masa da tuhumce-tuhumcen da ake masa.
Jihohi biyu ne dai a Amurka wato California da Texas suke neman Mr. El-Chapo din saboda zargin shigowa da muggan kwayoyi jihohin da yake yi.
Sau biyu dai ana kama Mr. Guzman dan shekaru 59 a duniya to sai dai yana sulalewa ya gudu.