Mata Sun Fara Gudanar Da Zanga-Zangogin Kin Jinin Donald Trump
https://parstoday.ir/ha/news/world-i16894-mata_sun_fara_gudanar_da_zanga_zangogin_kin_jinin_donald_trump
Rahotanni daga kasashe daban-daban na duniya suna nuni da cewa dubun dubatan mata ne suka fito kan titunan birane daban-daban na duniya a wani shirin zanga-zanga ta kasa da kasa ta kyamar sabon shugaban Amurka Donald Trump.
(last modified 2018-08-22T06:59:34+00:00 )
Jan 21, 2017 08:22 UTC
  • Mata Sun Fara Gudanar Da Zanga-Zangogin Kin Jinin Donald Trump

Rahotanni daga kasashe daban-daban na duniya suna nuni da cewa dubun dubatan mata ne suka fito kan titunan birane daban-daban na duniya a wani shirin zanga-zanga ta kasa da kasa ta kyamar sabon shugaban Amurka Donald Trump.

Rahotannin sun ce dubun dubatan mata ne ne suka fito a kasashen Birtaniyya,  Australia, New Zealand da kuma Japan don  gudanar da zanga-zangar kin jinin Shugaban Amurka Donald Trump din.

A Amurkan ma rahotanni sun ce ana sa ran akalla mutane 200,000 za su shiga cikin tattakin da dubban mata suka shirya gudanarwa a birnin Washington don nuna kyamar su ga shugaba Trimp din.

Hakan dai yana zuwa ne kwana guda da rantsar da shi da aka yi a matsayin shugaban Amurka na 45.