Wata kotu ta dakatar da Trump daga korar Musulmi
https://parstoday.ir/ha/news/world-i17129-wata_kotu_ta_dakatar_da_trump_daga_korar_musulmi
Wata alkali a babbar kotun tarayya ta Amurka ta bayar da umarnin dakatar da aiwatar da dokar da Shugaban Amurkan Donald Trump ya sanya wa hannu na na korar 'yan kasashen wajen da ke dauke da takardun izinin zama a Amurka.
(last modified 2018-08-22T06:59:36+00:00 )
Jan 29, 2017 02:21 UTC
  • Wata kotu ta dakatar da Trump daga korar Musulmi

Wata alkali a babbar kotun tarayya ta Amurka ta bayar da umarnin dakatar da aiwatar da dokar da Shugaban Amurkan Donald Trump ya sanya wa hannu na na korar 'yan kasashen wajen da ke dauke da takardun izinin zama a Amurka.

Rahotanni daga Amurkan sun ce kungiyar kare hakkin bil'adaman ta The American Civil Liberties Union (ACLU) ce ta shigar da karar inda ta bukaci da a hana aiwatar da wannan dokar da take ci gaba da fuskantar Allah wadai daga ciki da wajen Amurkan.

Kungiyar dai ta ce a halin yanzu akwai mutane kimanin 100 zuwa 200 da suke tsare a filayen jiragen saman Amurka saboda wadanda kuma suke da takardun izinin zama a Amurkan ko kuma ingantattun takardun 'yan gudun hijira, wanda a cewarta aiwatar da wannan umurnin kotun zai taimaka musu fita daga cikin wannan tsaka mai wuyan da suke ciki.

Rahotanni daga Amurkan sun ce bayan da mai shari'a Ann Donnelly ta fitar da wannan hukuncin mutane a filayen jiragen Amurkan inda mutane suke tsare sun ta shewa da nuna farin cikinsu kamar yadda kuma suka ci gaba da yin Allah wadai da wannan doka.