'Yan Biritaniya Na Son A Hana Trump Ziyartar Kasar
(last modified Mon, 30 Jan 2017 15:24:36 GMT )
Jan 30, 2017 15:24 UTC
  • Donald Trump ya ce yana kan bakarsa na hana baki shiga Amurka.
    Donald Trump ya ce yana kan bakarsa na hana baki shiga Amurka.

Sama da mutane milyan daya da dari biyu ne suka sanya hannu kan wata takardar koke domin hana sabon shugaban Amurka ziyartar kasar.

Takardar dai na neman ''Trump ya shiga Birtaniya a matsayinsa na shugaban Amurka, ba da sunan ziyarar aiki ba, don hakan zai jawo wa sarauniyar Ingila bakin jini''

Matsayin firaministar kasar ne na kin yin allawadai tunda farko da matsayin Donald Trump na hana musulmi shiga Amurka shi ne dai ya janyo suka da kuma neman hana ziyarar da ake sa ran Trump zai kai Biritaniya a cikin wannan shekara.

Theresa May, ita ce dai babbar jami'ar gwamnatin wata kasa data fara ganawa da shugaban Donald Trump, kuma ita ce ta sanar da ziyarar tasa lokacin da ta ziyarci Amurka a ranar Juma'a da ta gabata.

A gobe  Talata ne ake sa ran firaministar Biritaniyar Theresa May za ta tattauna wannan batu.

Shugabanin Kasashen Duniya dai na ci gaba da sukar matsayin Donald Trump na hana baki Musulmi shiga Amurka, dokar da tuni ta haifar da fito na fito a kasar.