Amurka: Donald Trump Ya Karawa 'Yan sandan Kasar Karfin Aiki.
https://parstoday.ir/ha/news/world-i17515-amurka_donald_trump_ya_karawa_'yan_sandan_kasar_karfin_aiki.
Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya rattaba hannu akan wasu sabbin dokoki 3 da su ka karawa 'yan sandan jahohi da tarayya karfin aiki.
(last modified 2018-08-22T06:59:39+00:00 )
Feb 10, 2017 07:24 UTC
  • Amurka: Donald Trump Ya Karawa 'Yan sandan Kasar Karfin Aiki.

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya rattaba hannu akan wasu sabbin dokoki 3 da su ka karawa 'yan sandan jahohi da tarayya karfin aiki.

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya rattaba hannu akan wasu sabbin dokoki 3 da su ka karawa 'yan sandan jahohi da tarayya karfin aiki.

Shugaban na kasar Amurka ya bayyana cewa; Karawa 'yansanda karfin aiki, ya zama wajibi saboda yadda ake samun karuwar aikata manyan laifuka. Dokokin da shugaban kasar ya rattaba hannu akansu sun kunshi sabuwar fassara ta manyan laifukan tarayya da kuma kara girman hukunci akan laifukan domin hana amfani da karfi akan 'yansanda.

A bisa wani rahoto, a cikin shekarar 2016 akn kashe 'yan sanda 135 a cikin fadin kasar ta Amurka, wanda shi ne mafi girma a cikin shekaru biyar na bayan nan.

Sai dai kuma shugaban na kasar Amurka bai yi la'akari ko ambaton daruruwan fararen hular da 'yansandan na Amurka kashe ba.