MDD Ta Kare Matsayinta Na Zabin Bafalastine Wakilinta A Libya
Babban sakatare na MDD, Antonio Guterres, ya kare matsayinsa na zaben tsohon firaministan Palestinu, Salam Fayyad, a matsyin wakilin na MDD a kasar Libya.
Wannan dai ya biyo bayan kin amuncewar da Amurka ta yi na naddin Mista Fayyad a wannan matsayin domin a cewarta MDD na fifita Palestinu akan kawarta Isra'ila.
Saidai a wata sanarwa daya fitar ta bakin kakakinsa a wannan Asabar, Mista Guterres ya MDD tayi wannan zabin ne saboda matsayinsa da kuma cancantarsa akan wannan matsayin.
Mista Stéphane Dujarric ya fada a sanarwar cewa MDD bata aiki da kasar da mutun ya fito kafin ta bashi matsayi, tana aiki ne gogewa mutun da kuma cancantarsa.
Shi dai Salam Fayyad dan shekaru 64 ya kasance tsohon fira ministan Palestinu daga shekara 2007 zuwa 2013 kana kuma ya taba zama ministan kudi na kasar har sau biyu, ya kuma jima yana aiki a wasu bankunan Amurka.
A Ranar Juma'a data gabata ce jakadiyyar Amurka a MDD, Nikki Haley ta kalubalenci nadin Salam Fayyad tare da cewa Amurka na adawa da matakin kasancewarta kasar da ba'a har yanzu ba'a amunce da Palestinu ba a matsayin kasa mai zamen kan ta.