Ficewar Britania Daga Tarayyar Turai Zai Dauki Fiye Da Shekaru Biyu
(last modified Fri, 17 Feb 2017 11:56:21 GMT )
Feb 17, 2017 11:56 UTC
  • Ficewar Britania Daga Tarayyar Turai Zai Dauki Fiye Da Shekaru Biyu

Shugaban majalisar zartarawa ta tarayyar Turai ya bayyana cewa ficewar Britania daga tarayyar Turai zai dauki akalla shekaru biyu cutar ana yi.

Jaridar Telegraph ta Britania ta nakalto Jean-Claude Juncker yana fadar haka a jiya Alhamis ya kuma kara da cewa, ba zai yu a cikin sa'o'i 24 a fayyece dangantakan kasar Britania da wadan nan kasashe ba. 

Jean-Claude Juncker ya kara da cewa ficewar britania daga tarayyar Turai yana bukatar a nata bangaren kadai ta sauya dokokin kasar kimani dubu 20,000 wadanda suke magana dangane da dangantakarta da tarayyar Turai.

Banda haka shugaban majalisar zartarwa da tarayyar Turai ya kara da cewa gwamnatin kasar Britania bata da hurumin kulla wasu yerjejeniyoyi da wasu kasashen duniya, ba tare da ta sauya wadannan dokoki ba.

Sai dai Priministan kasar Britania Theresa May ta tuni ta fara shirin cika sharuddan ficewa kasar daga Tarayyar ta Turai kamar yadda dokar Kungiyar EU ta 50 ta fayyace.