Ganawar Donald Trump Da Benjamin Netanyahu A White House
https://parstoday.ir/ha/news/world-i17748-ganawar_donald_trump_da_benjamin_netanyahu_a_white_house
A jiya ne Firayi ministan haramtacciyar kasar Isra’ila ya gana da shugaban kasar Amurka Donald Trump a fadar White House da ke birnin Washington a ziyarar da ya fara gudanarwa a kasar ta Amurka.
(last modified 2018-08-22T11:29:41+00:00 )
Feb 17, 2017 18:40 UTC
  • Ganawar Donald Trump Da Benjamin Netanyahu A White House

A jiya ne Firayi ministan haramtacciyar kasar Isra’ila ya gana da shugaban kasar Amurka Donald Trump a fadar White House da ke birnin Washington a ziyarar da ya fara gudanarwa a kasar ta Amurka.

Baya kammala ganawarsu sun gudanar da taron manema labarai na hadin gwiwa, inda Trump da Netanyahu suka bayyana cewa bangarorin Amurka da Isra’ila za su yi aiki kafada da kafada wajen tunkarar dukkanin kalubalen da ke a gabansu.

Netanyahu ya ce babbar matsala da take a matsayin babban kalu bale ga Isra’ila ita ce Iran da kuma shirinta da ya kira na kera makaman nukiliya, inda ya ce za su aiki tare da gwamnatin Amurka karkashin jagorancin Trump da kuma kasashen larabawa masu sassaucin ra’ayi domin tunkarar Iran, da kuma abin da ya kira ta’addancin muslunci, kamar yadda kuma Netanyahu ya jaddada wa Trump cewa kasashen larabawa masu sassaucin ra’ayi bas u da wata matsala da Isara’ila, bil hasali ma su abokan kawance ne a gare ta.

Shi ma a nasa bangaren Donald Trump a cikin kalamansa ya karfafa abin da Netanyahu ya fada, tare da jaddada cikakken goyon bayansa ga Isra’ila maras misiltuwa, duk kuwa da cewa ya kirayi Isra’ila da Palastinawa da cewa su yi sassauci a kan wasu matakai da suke dauka domin samun sulhu a tsakaninsu, kamar yadda kuma yaki ya matsayarsa kan batun mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin Quds daga Tel aviv.

A ranar Talata da ta gabata, kwana daya kafin ganawarsa da Netanyahu, Trump ya bayyana cewa baya daukar batun kafa kasar Palastinu mai cin gishin kanta a matsayin hanyar warware rikicin Isra’ila da Palastinawa, yana mai ishara da yin watsi da batun kafa gwamnatin Palastinawa mai cin gishin kanta wanda gwamnatin Obama da ma wasu daga cikin kasashen turai suke goyon bayan hakan.

Benjamin Netanyahu wanda ya kasance a cikin farin ciki maras misiltuwa bayan da Trump ya lashe zabe, daga bisani ya koma yin taka tsatsan dangane da batun na Trump, inda ya kirayi sauran jami’an Isra’ila da cewa su ma suka yin taka tsatsan matuka har sai an ga kamun ludayin Trump dangane da sha’anin Isra’ila, musamman ma bayan da Trump ya fara sauya kalamansa a kan batun dauke ofishin jakadancin Amurka daga Tel aviv zuwa Quds.

To koma dai yaya lamarin yake, a cewar Sheldon Adelson shugaban jaridar Yasra’il Hiyum, wanda bayahuden Amurka ne mai tsatsauran ra’ayi wanda kuma ya kashe kudi fiye da dala miliyan 125 domin yi wa Trump kamfe, ya bayyana cewa ganawar Trump da Netanyahu ta yi nasara, domin babban abin Netanyahu ke bukata shi ne gamsar da Trump a kan yin aiki kafada da kafada a tsakanin Isra’ila da Amurka da larabawa masu sassauci domin fuskantar Iran, wanda kuma tuni wasu daga cikin sarakunan larabawa da Trump ya zanta da su a kwanakin baya ta wayar tarho, suka tabbatar masa da cewa a shirye suke da a yi wannan aiki na hadin gwaiwa a tsakaninsu, kamar dai yadda Netanyahu ya gabatar masa.

Abin jira a gani dai yanzu shi ne, daga ina kawancen Amurka da Isra’ila da sarakunan larabawa masu sassauci zai fara aiki a kan Iran, domin kuwa ta fuskar soji dai ba abu ne mai sauki ba, domin kuwa tun daga barazanar da Trump ya yi da farko bayan gwajin makami mai linzami da Iran ta yi, da kuma ta sake yin wasu gwaje-gwajen ba a kara jin duriyar barazanar soji da Trump ya  yi a kan Iran ba, idan kuma ta fuskar takunkumin tattalin arziki ne, mafi yawan sauran kasashen turai ba a shirye suke su bi sahun Trump ba, saboda haka takunkmin zai takaita me kawai da Amurka da kuma sarakunan larabawa masu sassauci, wadanda kuma babu wata alaka mai karfi ta tattalin arziki da ta hada su da Iran, balantana Isra’ila wadda Iran ma ba ta amince da ita a matsayin kasa ba.