Amurka Ta Sake Kai Hari Kan Al-Qaida A Yemen
Mar 03, 2017 09:54 UTC
Rahotanni da Yemen na cewa jiragen yakin Amurka sun sake kai hari kan gidajen wasu mayakan Al-Qaida ciki har da gidan wani babban kwamandan kungiyar.
Kamar yadda wasu majiyoyi daga yankin suka tabbatarwa da kanfanin dilancin labaren AFP sun ce hare-haren sun rutsa da mutane da dama galibi mata da yara.
Mazauna yankin Yashbam sun ce sun kwana cikin zullumi sakamakon hare-haren.
Ko a jiya ma Amurka ta kai ire-iren wadanan hare-haren inda bayannai ke cewa an kashe wasu kwamandan kungiyar ta Al-Qaida a reshen kasashen larabawa su 12.
Tags