Zaben Faransa : Alain Juppe Ya Ce Ba Zai Tsaya Takara Ba
Tsohon fira-ministan Faransa, Alain Jupe, ya ce ba zai sake tsayawa takara ba a zaben shugabancin kasar na watan Afrilun dake tafe ba.
Hakan dai ya kawo karshen cece-kucen da ake yi na cewa zai maye gurbin Francois Fillon Filllon da ke fuskantar matsin lamba sakamakon zargin ya bai wa iyalansa aiki ba bisa ka’ida ba.
Mista Juppe dan shekaru 71 ya tabbatar a wani taron manema labarai cewa, ba zai tsaya takara ba a zaben shugabancin kasar ba.
Alain Juppe dai shi ne dan takara daya sha kaye a zaben fidda gwani na jam'iyyar ta 'yan Repablicain a watan Nowamba bara, kuma ana ganin ya yi hakan ne domin hada kan 'ya 'yan jam'iyar a yayin da zaben kasar ke karatowa.
Tuni dai wani bangare na kusoshin jam'iyyar masu ra'ayin rikau suka dawo da rakiyar Mista Fillon, wanda tuni wani zaben jin ra'ayin jama'ar kasar ya nuna cewa zai sha kaye tun zagayen farko a zaben na ranar 23 ga watan gobe.