Adawar Al'ummar Amurka kan sabuwar Dokar Trump dangane da 'yan hijra
Wasu Amurkawa sun bayyana adawar su kan sabuwar dokar da Shugaban kasar Donal Trump ya sanyawa hannu wacce ta haramtawa 'yan kasashe 6 na musulmi shiga Amurka.
A jiya Talata, Dariruwan mazauna garin Watsinton ne suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da wannan sabuwa doka inda suka yi tsuntsurundo a gaban babban ginin Ofishin dake kula da kare kan iyakar kasar inda suke bayyana adawar su kan sabuwar dokar da Shugaba Trump ya sanyawa hannu na hana wasu kasashen musulmi shida shiga cikin kasar.
Mahalarta zanga-zangar dai na rera taken cewa mu muna adawa da masu gyamar musulmi, sannan kuma sun bayyana wannan mataki a matsayin abin kunya ga Amurka.
Daya daga cikin mahalarta zanga-zangar ya bayyana cewa wannan sabuwar doka da Shugaba Trump ya sanyawa hannu na nufin cewa yana goyon bayan masu gyamar baki da gyamar musulinci a kasar
Wannan Sabuwar Doka dai ta haramtawa 'yan kasashen Iran, Siriya, Yemen, Somaliya, Sudan da kuma Libiya shiga cikin kasar Amurka har zuwa kwanaki 90. magabatan Amurkan sun ce sun dauki wannan mataki ne saboda dalilai na tsaro musaman ma hana kwararen 'yan ta'adda shiga kasar.