Sojojin Siriya Sun Yi Nasarar Kashe Gungun 'Yan Ta'adda Da Dama
Sojojin gwamnatin Siriya sun kai hari kan wani gungun 'yan ta'adda a yankin garin Diru-Zur da ke gabashin kasar, inda suka kashe gungun 'yan ta'adda masu yawa.
Kamfanin dillancin labaran kasar Siriya "SANA" ya sanar da cewa: Sojojin Gwamnatin kasar sun kai hari kan wani gungun 'yan ta'addan kungiyar Da'ish ta suke kokarin kutsawa cikin garin Diru-Zur a shiyar gabashin kasar, inda suka tarwatsa takokin yaki da kananan motocin da 'yan ta'adda suke ciki gami da tankokin mai da suke musu rakiya.
Har ila yau jiragen saman yakin sojojin Siriya sun yi luguden wuta kan gungun 'yan ta'addan kungiyar Da'ish a kauyukan Ayash, Baghlilah, Husainiyya da gefen grin Sardah da Makabir a garin na Diru-Zur, inda suka kashe 'yan ta'adda da dama tare da tarwatsa motocin yakinsu.