Amurka Ta Kori 'Yan Somaliya Kimanin 70 Daga Kasar
Ministan harkokin wajen Somaliya Abdirisak Omar Mohamed, ya tabbatar da cewa, kimanin 'yan kasar guda 70 da aka kora daga Amurka sun isa Mogadishu, babban birnin kasar.
Wannan dai a cewar Mista Abdirisak shi ne karo na biyu da Amurka ta kori 'yan kasar Somaliya daga kasarta, ya ce mutanen sun zauna a cibiyar tsare 'yan gudun hijira na kasar Amurka tsawon shekaru biyu, amma ba su samu iznin zama a kasar ba saboda sharudan doka.
Rahotanni sun bayyana cewa, ko a karshen watan Junairun daya gabata, Amurkar ta kori 'yan kasar Somaliya 90 daga kasarta.
A ranar 21 ga watan Fabrairun da ya gabata ne, ma'aikatar tsaron Amurka ta fidda wasu takardun doka guda biyu, inda ta kara adadin 'yan gudun hijira da za ta kora daga kasar, wadanda suka shiga kasar ba bisa doka ba.
Somaliya dai na daga cikin jerin kasashen da Amurka ta haramtawa mutanenta shiga kasar a sabuwar dokar takaita baki shiga kasar ta shugaba Donald Trump.