Muftin Masar: 'Yan Ta'addan Na Murguda Koyarwar Musulunci Don Cimma Burinsu
Babban muftin kasar Masar, Sheikh Shawki Ibrahim Abdel-Karim Allam ya bayyana cewar kungiyoyin 'yan ta'adda suna mummunar amfani da koyarwar addinin Musulunci da kuma murguda su wajen cimma manufofinsu.
Kamfanin dillancin labaran RASA ya jiyo babban muftin kasar ta Masar Shawki Ibrahim Abdel-Karim Allam yana fadin cewar a halin yanzu kungiyoyin 'yan ta'adda suna amfani da wasu koyarwar Musulunci wajen janyo hankulan jama'a zuwa gare su da kuma haifar da sabani tsakanin al'umma.
Har ila yau kuma yayin da yake ishara da tushen irin wannan yanayin cikin tarihin Musulunci, babban muftin na kasar Masar yayi ishara da yadda Khawarijawa a lokacin halifancin Imam Ali (a.s) suka yi amfani da daga Alkur'ani mai girma da kalmar cewa "Babu wani hukunci in ba na Allah ba' wajen cimma bakaken manufofinsu.
A saboda haka Shehin malamin ya kirayi matasa da su yi taka tsantsan da irin wadannan mutane da suke amfani da Musulunci wajen janyo hankulansu zuwa ga bata.