Ministan cikin gidan Faransa ya yi murabus
https://parstoday.ir/ha/news/world-i18728-ministan_cikin_gidan_faransa_ya_yi_murabus
Ministan cikin gidan kasar Faransa Bruno Le Roux ya sauka daga mukaminsa, sa’o’i kadan bayanda babban lauyan gwamnatin kasar, ya sanar da fara bincike kan zargin badakalar ayyukan bogi da ake wa ministan, na baiwa yayansa mata mukaman mataimakansa a majalisar dokokin kasar, a lokacin da yake dan majalisa.
(last modified 2018-08-22T06:59:51+00:00 )
Mar 22, 2017 07:55 UTC
  • Ministan cikin gidan Faransa ya yi murabus

Ministan cikin gidan kasar Faransa Bruno Le Roux ya sauka daga mukaminsa, sa’o’i kadan bayanda babban lauyan gwamnatin kasar, ya sanar da fara bincike kan zargin badakalar ayyukan bogi da ake wa ministan, na baiwa yayansa mata mukaman mataimakansa a majalisar dokokin kasar, a lokacin da yake dan majalisa.

Murabus din Ministan na zuwa ne a yayin da ya raga wata guda kacal da zaben Shugaban kasar Faransa, kuma Masana na ganin cewa yin murabus din ministan cikin gidan na iya yiwa zaben illa, a cikin 'yan watanin nan ana zarkin wasu 'yan takarar Shugaban kasar da irin wannan laifi.

Yanzu haka dai lauyan gwamnatin Faransa, mai binciken badakalar kudi ya saka Bruno Le Roux, a jerin takwarorinsa da yake zargi da irin wannan laifi da suka hada da François Fillon dan takarar jam’iyyar Republican ta ‘yan adawa , na bawa matarsa aikin bogi na mataimakiyarsa a harkokin majalisar dokoki a lokacin da yake rike da mukamin Firaministan kasar daga shekarar 2008 zuwa da 2012. da kuma uwargida Marine Le Pen, da ita ma ake zargi da bada aikin bogin, amma ita nata a majalisar dokokin kungiyar tarayyar turai EU.