Hukumar Makamashin Nukiliya Ta yi Koke Akan Rashin Cikakken Kasafin Kudi.
https://parstoday.ir/ha/news/world-i18744-hukumar_makamashin_nukiliya_ta_yi_koke_akan_rashin_cikakken_kasafin_kudi.
Yokiya Amano ya ce; Idan ba a samar da kasafin kudin ba, to ci gaba da sa ido akan cibiyoyin Nukiliyar Iran yana cikin hatsari.
(last modified 2018-08-22T11:29:51+00:00 )
Mar 23, 2017 06:32 UTC
  • Hukumar Makamashin Nukiliya Ta yi Koke Akan Rashin Cikakken Kasafin Kudi.

Yokiya Amano ya ce; Idan ba a samar da kasafin kudin ba, to ci gaba da sa ido akan cibiyoyin Nukiliyar Iran yana cikin hatsari.

Yokiya Amanu ya ce; Idan ba a samar da kasafin kudin ba, to ci gaba da sa ido akan cibiyoyin Nukiliyar Iran yana cikin hatsari.

Kamfanin dillancin labarun Associated Press ya ambato babban sakayaren  hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa, ya ce; Sanya ido akan cibiyoyin Nukiliyar Iran yana cikin hatsari, sai idan  kasashe mambobi da su ka hada da Amurka, sun kara yawan kudaden da su ke bayarwa.

Amanu ya ci gaba da cewa a shekarar 2018, hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa, za ta bukatu da karin kasafin kudinta da kaso 2/1, wanda zai kai dala miliyan 370.

A makon da ya shude ne dai Amanu ya fitar da rahoto akan shirin makamashin na Iran, da ya bayyana da cewa; Na sulhu ne.