Masar : Al-Sisi Zai Gana Da Trump Na Amurka
https://parstoday.ir/ha/news/world-i19026-masar_al_sisi_zai_gana_da_trump_na_amurka
Bayan shafe shekaru hudu na rashin jituwa da Amurka, shugaba Abdel Fattah al-Sissi na Masar zai gana da takwaransa na Amurka Donald Trump.
(last modified 2018-08-22T06:59:54+00:00 )
Apr 01, 2017 06:44 UTC
  • Masar : Al-Sisi Zai Gana Da Trump Na Amurka

Bayan shafe shekaru hudu na rashin jituwa da Amurka, shugaba Abdel Fattah al-Sissi na Masar zai gana da takwaransa na Amurka Donald Trump.

Ana sa ran dai bangarorin zasu gana ne a ranar Litini mai zuwa a Washington, inda zasu tattauna kan batutuwa da dama cikin har da farfado da alakar dake tsakanin kasashen biyu.

Batun yaki da 'yan ta'addan ( IS) dake barazawa kasar ta Masar da kuma rikicin Palestine da Isra'ila na daga cikin batutuwan da bangarorin za su tattauna.

Ziyara Al-sisi na Masar na zuwa ne kwana biyu bayan wace sarki Abdallah na Jodan ya kai Amurka, inda suka tattauna kan rikicin Palestinu da Isra'ila.

Masar da Jodan ne dai kasashen Larabawan da suka daddale yarjejeniyar zamen lafiya da mahukuntan yahudawan mamaya na Isra'ila.