Sharhi: Ziyarar Sakataren Wajen Amurka A Turkiya
A ranar Alhamis da ta gabata ce sakataren harkokin wajen kasar Amurka Rex Tillerson ya isa birnin Anka na kasar Turkiya, inda ya gana da shugaban ta Turkiya Rajab Tayyib Erdogan.
Ganawar da ta gudana tsakanin Tillerson da kuma Rajab Tayyib Erdogan an yi ta ne a cikin sirri matuka, inda babu ko daya daga jami’an gwamnatin Amurka da suke tare da Tillerson da ya halarci ganawar, yayin da haka lamarin a bangaren Turkiya, inda Errdogan da kuma ministan harkokin wajen Trkiya Jawish Auglo ne kawai suka kasance a wurin, inda Jawish Auglo yake a matsayin mai tafinta a tsakanin Tillerson da kuma Erdogan
Tattunawar dai ta mayar da hankali ne a kan batun yaki da ta’addanci a Syria, da kuma yadda bangarorin biyu za su iya yin aiki tare, musamman kan batun shirin fitar da ‘yan ta’addan ISIS daga birnin Raqqah da ke gabashin kasar ta Syria, wanda a halin yanzu karkashin ikon ‘yan ta’addan ISIS.
A tattaunawar wadda ta dauki tsawon sa’oi, baya ga batun ayyukan hadin gwiwa tsakanin Amurka da Turkiya a fagen yaki da ‘yan ta’adda a Syria, an kuma tabo batun yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara a kasar ta Turkiya a cikin shekara ta 2016 da ta gabata, kamar dai yadda ministan harkokin wajen Turkiya Jawish Auglo ya sheda ma manema labarai, inda y ace sun kalli wani hoton bidiyo kan yadda yunkurin juyin mulkin ya kasance.
A baya-bayan nan musamamn bayan lashe zaben shugabancin kasar Amurka da Donald Trump ya yi, Erdogan ya bude shafin rikici tsakaninsa da kasashe da dama, da suka hada har da manyan kasashen turai irin su Jamus, Holland, Swizland da sauransu, sakamakon hangen dala a tunaninsa na neman samun wurin zama a cikin sabuwa siyasar da ke tafiyar da fadar white house a halin yanzu a karkashin Donald Trump.
Erdogan na son ganin ya hada wani kawance tsakaninsa da sabuwar gwamnatin Amurka, sabanin gwamnatin Obama wadda ta yi jifar ‘yar mage da shi, inda yake hankoron ganin ya hada kai da Amurka domin ganin an kwato birnin raqqah na Syria daga ‘yan ta’addan ISIS, domin kara tabbatar da samuwarsa a cikin Syria, da nufin jifar tsuntsu biyu da dutse daya, inda hakan zai ba shi damar tunkarar Kurdawan da yake kallonsu a matsayin barazana a gare shi da suke da karfi a cikin Syria, a lokaci guda kuma hakan zai ba shi damar ya shigo cikin Syria tsamo-tsamo wadda ya kwashe shekaru 6 yana mafarkin kifar da gwamnatinta.
To sai dai furucin da ke fitowa daga bakunan wasu manyan jami’an tsaron Amurka a Pentagon dangane rashin tabbaci kan ko Erdogan zai iya zama abokin kawance wajen kwato Raqqah, hakan ya sanya shi a cikin rudani, inda suke cewa sun fi samun tabbaci da natsuwa tare da abokan kawancensu na mayakn Kurdawa da suke yaki a halin yanzu a cikin lardin Raqqa, musamman ganin irin yadda mayakan ISIS suka yi wasan kura da sojojin Turkiya a garin Bab da ke kan iyakar Syria da Turkiya, wanda rashin samun wannan tabbaci daga Amurka, zai rusa lissafin da Erdogan ya yi a hankoronsa na fadada samuwarsa a fagen siyasar nuna dantse da masu karfi na duniya ke yi a Syria, domin kuwa ikon fada a ji da Erdogan yake da shi a kan ‘yan ta’adda a kasar ta Syria, shi ne babban makamin da ya dogara da shi wajen cimma burinsa na siyasa tsakaninsa da kasashen turai da ma wasu kasashen da ya bude shafin rikici da su a baya-bayan nan.