Koriya Ta Arewa Ta Yi Barazanar Maida Martani
Koriya ta Arewa ta ce zata maida martani idan har kasahen duniya suka yunkura karkafa takunkuman da suka kakaba mata akan shirinnukiliyarta.
Wannan barazanar Koriya ta Kudu na zuwa ne kwana guda kalaman shugaban Amurka Donald Trump na cewa yana shirye wajen kawo karshen matsalar Koriya ta Arewar ba tare da taimakon kasar Sin ba.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin soma wani atisayan soji na kasashen Japon, Koriya ta Kudu da kuma Amurka a yankin mai nufin kawar da duk wata barazana ta harbe-harben makamai masu linzami na Koriya ta Arewar.
Saidai a cewar kakain ma'aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa wannan atisayan na kawacen kan iya rura wutar rikici a yankin, kana kuma a cewar sabatun cewa Amurka ta hana Koriya ta Arewa shirinta na nukuliya ''mafarki ne''.