Goyon Bayan Kungiyar Turai Na Magance Rikicin Siriya ta Hanyar Siyasa
(last modified Fri, 07 Apr 2017 17:53:13 GMT )
Apr 07, 2017 17:53 UTC
  • Goyon Bayan Kungiyar Turai Na Magance Rikicin Siriya ta Hanyar Siyasa

Babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Federica Mogherini ta tabbatar da cewa Kungiyar Turai na goyon bayan magance rikicin kasar Siriya ta hanyar Siyasa.

Kamfanin dillancin labaran kasar Iran ya nakalto Babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Federica Mogherini cikin wani bayyani da ta fitar a wannan Juma'a ta ce wajibi ne a bi hanyoyin tattauwa da kuma Siyasa domin magance rikicin kasar Siriya.

Jami'ar ta kara da cewa Kungiyar Turai ta aminta da cewa rikicin Siriya ba za a iya magance shi ba ta hanyar karfin Soja, kuma kungiyar na goyon bayan hadin kai da kuma 'yancin kasar Siriya.mafita guda cilo na magance rikicin , shi ne aiki da kudiri mai lamba 2254 na kwamitin tsaron MDD wanda ya yi lamini na sulhu da kuma dawo da tsaro a kasar tare kuma da rusa kungiyar ISIS da kuma duk wasu kungiyoyin 'yan ta'adda dake cikin jerin kungiyoyin 'yan Ta'adda na MDD

Wannan Sanarwa na zuwa ne bayan harin bazata da kasar Amurka ta kai Sansanin Sojin Saman Siriya na Shayrat dake cikin jihar Humus da makamai masu Lizzami har 59 a jijjifin Safiyar Yau Juma'a.