Amurka : Trump Ya Gana Da Sakatare Janar Na MDD
Shugaban Amurka Donald Trump ya gana da sakatare janar na MDD, Anatonio Guterres, wace kuma iata ce ganawarsu ta farko tun bayan kama mulki a watan Janairu.
Bangarorin biyu dai sun tattauna kan batutuwa da dama ciki har da huldar ta tsakanin AMurka da MDD a cewar kakakin MDD Stephane Dujarric.
A cewar Dujaric, ganawar ta tsakanin bangarorin biyu ta yi armashi, inda har ma sukayi alkarin yin wata ganawa nan gaba.
MDD dai ta damu akan matakin sabuwar gwamnatin Amurka na rage yawan talafin da take baiwa MDD.
Dama kafin hakan Donald Trump ya gana da wakilan kasashe mambobin kwamitin tsaro na MDD, inda suka tabo batutuwa da suka hada da rikicin Syria, da barun Koriya ta Arewa da kuma rikici na tsakanin Isra'ila da Palasdinu.