Sharhi : Zaben Shugaban Kasa A Faransa
Zaben shugaban kasar Faransa na 2017 shi ne irinsa na farko da ake gudanarwa karkashin dokar ta baci da kuma kwararen matakai na tsaro, yayin da ake ci gaba da fargaban harin ta’addanci bayan kashe dan sanda a birnin Paris.
Faransawa kimanin Miliyan 46 ne ke kada kuri'a a zaben zagayen farko, sai dai masu sharhi sun bayyana cewa, harin na ranar Alhamis da ta gabata, zai iya yin tasiri dangane da fitowar jama’a don kada kuri’unsu a zaben.
'Yan takara 11 ne fafatawa a zaben na yau Lahadi, amman daga cikinsu biyar ne ake ganin za su kai labari a zaben, wadanda suka da Fransois Fillon, Benoit Hamon, Uwar gida Marine Le Pen, Emmanuel Macron, Jean-Luc Melenchon.
Matsayin ilahirin ‘yan takarar kasar kan kungiyar EU da baki da kuma mu’ammala da al’ummar Musulmi na da matukar mahimmanci a siyasar Faransa.
Saidai da dama daga cikin hankulan Faransawa sun karkata kan yan takara biyu Emmanuel Macron mai zaman kansa da ke da ra’ayin zaunar da Faransa a cikin kungiyar ta Tarrayar Turai da kuma Uwargida Marine Le Pen ta jam’iyyar Front National mai adawa da ci gaban zaman kasar a EU.
Mista Maccron ya ce ko shakka babu, kasancewarsa cikakken Bafaranshe ya fi sha’awar hada kai da sauran kasashen Turai don ciyar da nahiyar gaba.
Ita kuwa Mme Le Pen cewa ta yi, in har ta lashe zaben shugabancin kasar, za ta fitar da Faransa cikin kungiyar kasashen Turai.
A shekarar 2012, Marine Le Pen ta zo ta uku a zaben shugabancin kasar da kashi 17. 90 na kuri’un da aka kada, wannan dai shi ne karo na biyu da Le Pen ke sake nuna sha’awar zama shugabar kasar Faransa.
Marine Le Pen ta na da matsanancin ra'ayin rikau da kuma adawa da 'yan gudun hijira, da baki ga kuma nuna kyama ga wasu al’addu na musulunci da ta ce, sun yi hannun riga da al’addar Faransawa.
Wani abu dake daukan hankali a zaben na faransa shi ne kashi 30% na masu kada kuri’a asalinsu baki ne kuma kashi 2 cikin 5 na su sun fito daga Afrika ne, kuma da dama cikinsu sun ce zasu zabi jam’iyyar FN ta Marine le Pen, duk da manufofinta kan baki.
Shi ma Jean-Luc Melenchon da ke ci gaba da samun karbuwa, na adawa da zaman Faransa a Turai, yayin da ya ce, in har ya ci zaben, zai bukaci a gudanar da zaben raba gardama kan batun zama a EU.
Francois Fillon kuwa, da ke takara a karkashin inuwar jam’iyyar Conservateur, na goyon bayan Tarayyar Turai, sai dai yana adawa da salon tsarin tattalin arzikin kungiyar.
Dan takara a jam’iyya mai mulki, Benoi Hamon shi ma dai na adawa da tsare-tsaren EU duk da dai bai ce, in har ya ci zaben zai fidda kasar daga cikin kungiyar ba.
Batun tattalin arziki da rashin aiki da kuma tsaro na daga cikin abubuwa da faransawa ke fatan ganin an magance.
Duk da cewa kasar Faransa ta shirya tsaf domin kada kuri’ar shugaban kasa, sai dai har yanzu babu hasashen wanda zai iya nasara, al’amari irinsa na farko a tsawon shekaru.
Saidai wani hasashe ya nuna cewa dan takara Emanuelle Maccron da Marine Le Pen ne za su fafata a zaben shugabancin kasar zagaye na biyu.
'Yan takara biyu da sukayi nasara a zaben na yau, sune zasu fafata a zagaye na gaba da za’a gudanar a ranar 7 ga Watan Mayu mai zuwa.