An Gunadar Da Zaben Faransa Cikin Kwararan Matakan Tsaro
Al'ummar kasar Faransa sun gudanar da zaben Shugaban kasa cikin kwararan matakan tsaro kalkashin dokar ta baci a fadin kasar baki daya.
Rahotanni dake fitowa daga kasar Faransa sun tabbatar da cewa duban jami'an tsaro ne aka girke a manyan buranan kasar domin bayar da kariya ga Al'ummar kasar dake kada kuri'in su.
Da misalin karfe takwas na safiyar yau agogon Faransa ne aka bude rumfunan zaben a dukkanin fadin kasar, yayin da kasashen duniya ke ci gaba da sanya ido kan yadda zaben ke gudana.
Ma’aikatar cikin gidan Faransa ta ce, zuwa yammacin ranar Lahadi, an samu kusan kashi 69.42 na jama’a da suka fito, don kada kuri’unsu, adadin da ya kusan kamo wanda aka samu a zagayen farko na zaben kasar na shekarar 2012, in da a wancan lokaci aka samu kashi 70. 59.
Wata kuri’ar jin ra’yin jama’a ta nuna cewa, Marine Le Pen ta jam’iyyar National Front da Emmannel Macron mai zaman kansa da Francois Fillon mai matsakaicin ra’ayi da kuma Jean Luc Malenchon mai ra’ayin rikau na kan gaba a zaben na yau.