Faransa : Maccron Ya Samu Goyan Bayan Hollande
Shugaban Faransa mai barin gado Francois Hollande ya sanar da matakin marawa Emmanuel Macron baya a zaben shugaban kasar zagaye na biyu da za a gudanar a ranar 7 ga watan Mayu mai zuwa.
Shugaba Hollande ya bayyana hadarin da ke tattare da zaben Marine Le Pen mai tsattsauran ra’ayin rikau data zo ta biyu a zaben shugaban kasar zagaye na farko daya gudana a ranar Lahadi data gabata.
Hollande ya ce Macron zai kada wa kuri’arsa tare da bayyana cewa zaben Le Pen barazana ce ga makomar Faransa a Tarayyar Turai.
Sakamakon din-dindin na zaben ya nuna cewa dan takara jam'iyya mai matsakaicin ra'ayi ne Emanuelle Maccron ya lashe zaben zagayen farko da kashi 24.01% yayin da 'yar takara 'yar takara mai tsattsaurar ra'ayi ta jami'yyar FN, Marine Le Pen ke biye masa da kashi 21.3% na kuri'un da aka kada.
Sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a na ci gaba da tabbatar da cewa Macron zai iya lashe zaben a zagaye na biyu da kusan kashi 60%.