Amurka: Iran Ita Ce Babbar Matsalarmu A Yankin Gabas Ta Tsakiya
(last modified Wed, 26 Apr 2017 16:57:58 GMT )
Apr 26, 2017 16:57 UTC
  • Amurka: Iran Ita Ce Babbar Matsalarmu A Yankin Gabas Ta Tsakiya

Tun a ranar Laraba da ta gabata ce sakataren tsaron Amurka James Mattis ya fara gudanar da wani rangadi a yankin gabas ta tsakiya, inda ya fara yada zango a birnin Riyadh na kasar Saudiyya.

Bayan isarsa birnin Riyadh fadar mulkin masarautar Al saud, sakataren tsaron Amurka James Mattis wanda ake yi wa lakabi da mahaukacin kare, ya gana da manyan jami’an masarautar Al Saud, da suka hada da sarkin masarautar Salman bin Abdulaziz, da kuma ministan tsaron masarautar Muhammad bin Salman bin Abdulaziz.

Bangarorin biyu na Amurka da Saudiyyah sun tattauna da suke da matukar muhimmanci a wurinsu, da suka hada da yadda za su hada karfi da karfe domin tunkarar Iran, saboda abin da suka kira matsalar da Iran take kawo musu a yankin gabas ta tsakiya, da kuma batun kasar Syria, wanda dukkanin kasashen biyu suna da hanu wajen kunna wutar wanann rikici da kuma daukar nauyinsa.

Baya ga haka kuma sakataren harkokin wajen Amurka  ya tattana batun sayarwa Saudiyya da makamai, wanda hakan na daya daga cikin babban abin da ya kara karfafa kawancen Saudiyya da Amurka a tarihin alakarsu, inda Saudiyya kan yi Amurka cinikin makamai na daruruwan biliyoyin daloli fiye da kowace kasa ta duniya, wanda kuma Amurka ba za ta taba yin wasa da hakan ba.

Bayan Saudiyya James Mattis ya nufi masar, inda ya gana da shugaba Sisi, tare da jaddada cewa Amurka za ta taimaka ma Masar wajen ganin ta fuskanci matsalar tsaro da ke addabatrta a halin yanzu.

Daga nan kuma Mattis ya wuce zuwa birnin Tel Aviv na haramtacciyar kasar Isra’ila, inda a can ma suka tattuna batutuwa da suka tattauna tare da mahukuntan saudiyya, inda dukkanin bangarorin uku, Amurka, saudiyya da kuma Isra’ila, suka hadu a kan cewa Iran ita ce matsala kuma ta zama karfen kafa ga manufofinsu a yankin gabas ta tsakiya.

Wannan mahanga ta bai daya tsakanin Amurka, Saudiyya da kuma Isra’ila a kan Iran, ita ce abin da wakiliyar Amurka a majalisar dinkin duniya ta yi wa kwamtin tsaro bayani, a zaman wata-wata da yake gudanarwa domin tattauna batutuwa da suka shafi yankin gabas ta tsakiya, inda ta ce lokaci ya yi da kwamitin tsaro zai mayar da hankali kaco kaf a kan Iran da Hizbullah dangane da duk wasu matsaloli da suka shafi gabas ta tsakiya, maimakon kallon Isra’ila da dora mata alhakin matsalolin da ake fama da su a yankin.

To ko ma dai ya lamarin yake, abin da ke faruwa ba bako ba ne ga masu bin diddigin siyasar duniya, domin kuwa manufar Amurka ba za ta taba canjawa a kan kasar Iran ba, matukar dai Iran za ta ci gaba da zama kasa mai ‘yancin siyasa da bata yin amshin shata ga Amurka, bayan haka kuma manufofin Donald Trump a kan Iran ya riga ya bayyana su tun kafin ya ci zaben kasar Amurka, duk kuwa da cewa duk duniya ta ga yadda su kansu Amurkawa da ma wasu gwamnatocin nahiyar turai, suke nuna adawa da wannan salo na bakar siyasar irin ta Donald Trump, wadda ba za ta haifarwa duniya da ita kanta Amurka da mai ido ba.