Paparoma Francis Zai Fara Ziyara A Masar
https://parstoday.ir/ha/news/world-i19888-paparoma_francis_zai_fara_ziyara_a_masar
A wani lokaci idan an jima ne Paparoma Francis, jagora mabiya darikar Katolika zai fara wata ziyara ta kwanaki biyu a birnin Alhakira na kasar Masar.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Apr 28, 2017 06:32 UTC
  • Paparoma Francis Zai Fara Ziyara A Masar

A wani lokaci idan an jima ne Paparoma Francis, jagora mabiya darikar Katolika zai fara wata ziyara ta kwanaki biyu a birnin Alhakira na kasar Masar.

Ana sa ran Paparoman zai yi amfani da wannan damar don tattaunawa da babban Limamin sunni na Al'Azhar akan abunda ya shafi hakuri na zamen tare.

An dai tsauraren kwararen matakai na tsaro a gabanin ziyayar a wuraren ibada da titunan da jagoran 'yan katolikan zai bi. 

Wannan ziyar ta Paparoma Francis na zuwa ne bayan hare-haren da kungiyar 'yan ta'addan IS mai da'awar jihadi don kafa daular islama a kasashen Iraki da Sham (Syria) ta kai kan cocin Kifdawa a ranar 9 ga watan Afrilu wanda ya hadasa mutuwar mutane 45.