Tarayyar Turai Ta Tsananta Tsarin Tattanawa Na Ficewar Britania Daga Kungiyar
Kungiyar tarayyar turai ta tsananta shirin tattaunawa da kasar Britanina don ficewarta daga tarayyar kamar yadda mutanen kasar suka bukata a zaben raba gardama na shekarar da ta gabata
Tashar television ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa shuwagabannin kasashe 27 na tarayyar Turai sun tsananta tsarin tattaunawa da kasar Britania don ficewarta daga tarayyar a wani taron da suka gudanar a birnin Brussses na kasar Beljuim a jiya Asabar.
Labarin ya kara da cewa tarayyar ta Turai tana bukatar tabbaci mai inganci kan makomar yayan kasashen 27 wadanda suke zaune a kasar Britania bayan ficewarta. Banda haka shuwagabannin na tarayyar Turai sun bukaci kasar Britania ta biya wasu makonan kudade sanadiyyar ficewarta daga tarayyar.
Har'ila yau shugaban tarayyar ta Turai ean-Claude Juncker ya tabbatar da cewa zasu shiga tattaunawa mai zafi tare da kasar Britania a shirinta na ficewa daga kungiyar nan gaba.