Ministan Harakokin Wajen Jamus Ya Kai Ziyara Hedkwatar Kungiyar AU
https://parstoday.ir/ha/news/world-i20016-ministan_harakokin_wajen_jamus_ya_kai_ziyara_hedkwatar_kungiyar_au
Ministan harkokin kasashen wajen Jamus Sigmar Gabriel ya bayyana cewa akwai bukatar kawo sauyi a alakar da ke tsakanin kasashen nahiyar Afirka da na nahiyar Turai.
(last modified 2018-08-22T07:00:03+00:00 )
May 03, 2017 01:10 UTC
  • Ministan Harakokin Wajen Jamus Ya Kai Ziyara Hedkwatar Kungiyar AU

Ministan harkokin kasashen wajen Jamus Sigmar Gabriel ya bayyana cewa akwai bukatar kawo sauyi a alakar da ke tsakanin kasashen nahiyar Afirka da na nahiyar Turai.

Gabriel ya bayyana hakan ne  birnin Addis Ababa a lokacin da ya kai ziyara kasar Habasha,  jim kadan bayan da ya baro kasar Somaliya, inda ya ce ya zama dole kasashen Turai su hada kansu tare da yin magana da murya guda kan batu na tsare-tsarensu a kasashen Afirka, wanda ya ce a yanzu akwai tsare-tsare mabanbanta da kasashen ke yi kuma bakinsu ya rabu yana mai cewa:"Mafi yawa kasashen na bin son zuciyarsu ne, su kare manufofinsu kawai a Afirka. Wasu lokutan abin kan zama bibiya irin na ayyukan lokacin  mulkin mallaka."

Minista Gabriel ya kuma ziyarci shelkwatar AU, inda ya gana da Moussa Faki Mahamat sabon shugaban hukumar da kalamansu  ya zo daya kan adawa da kafa sansanoni na 'yan gudun hijira a arewacin Afirka, matakin da suka ce ba zai magance batun kwararar 'yan gudun hijira ba.

Ya  ce dole shugabannin Afirka su zama masu adalci, ta yadda idan an ba da tallafi  zai rinka kai wa ga wadanda suka dace su samu. Ya kuma yi kira na samar da sauyi a siyasar kasar ta Habasha da ke karkashin dokar ta baci bayan zanga-zangar 'yan adawa.