Rahotanni Na Nuna Cewa Emmanuel Macron Ya Lashe Zaben Shugaban Faransa
Rahotanni daga kasar Faransa na nuni da cewa dan takara mai sassaucin ra'ayi Emmanuel Macron ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a yau din nan duk kuwa da karancin fitowar masu kada kuri’a da aka fuskanta a zaben na yau.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo wasu majiyoyin suna cewa Emmanuel Macron din ya samu kashi 65% na kuri'un da aka kada din alhali ita kuma abokiyar karawarsa mai tsaurin ra'ayi Marine Le Pen ta samu kashi 35% na kuri'un da aka kada din.
Kamfanin dillancin labaran na Reuters ya ce wannan sakamakon dai ba sakamako ne na karshe ko kuma a hukumance ba.
Idan dai har aka tabbatar da wannan sakamakon to Mr. Macron dan shekaru 39 a duniya zai zamanto shugaban Faransan mafi karancin shekaru tun bayan Louis Napoleon Bonaparte, wanda ya zama shugaban Faransan a shekarar 1848 yana dan shekaru 40 a duniya.
Zaben dai ya yi matukar daukar hankulan kasashen duniya musamman saboda irin bambancin manufofi da ke tsakanin 'yan takarar biyu wadanda suka yi hannun riga da juna, sannan kuma da irin rawar da sakamakon zaben zai taka dangane da makomar Tarayyar Turai, musamman bisa la'akari.
Wani lamari kuma da ya kara janyo hankali a zaben na yau shi ne cewa shi ne karon farko a shekaru 60 da ake gudanar da zaben zagaye na biyu ba tare da ‘yan takarar manyan jam’iyyun siyasar kasar guda biyu ba.