Tarihin Sabon Shugaban Faransa Emanuelle Macron
An haifi Emmanuel Jean Michel Frederic Macron a ranar 21 ga watan Disamban shekarar 1977 a Amiens da ke arewacin Faransa.
A shekara 2004 ne Mista Macron ya kammala karatunsa a ma'aikatar koyar da aikin gudanarwa ta ENA inda ya samu digiri a fannin, kana kuma ya zama Sufeto na kudi kafin daga bisani ya zama ma'aikaci da kuma shiga harkokin banki a 2008.
Ya kasance mamba a jam’iyyar Socialist tsakanin shekarar 2006 zuwa 2009, inda aka nada shi a matsayin babban magatakardar jam’iyyar a lokacin gwamatin Francois Hollande ta farko, wato a shekarar 2012, kafin daga bisani ya rike mukamin Ministan tattalin arzikin da masana’antu a shekarar 2014.
Macron mai shekaru 39 ya yi murabus daga mukamnin siyasa a bara don kaddamar da shirinsa na tsayawa takara a zaben 2017.
A ranar 16 ga watan Nuwamban bara ne, Macron ya ayyana manufarsa ta neman maye kujerar shugaba Francois Hollande mai barin gado, bayan shafe dokon lokaci na kiki-kaka akan hakan.
Macron ya kasance daya daga cikin yan takara 11 da suka tsaya takara a zaben shugabancin kasar ta faransa zagayen farko na ranar 23 ga watan Afrilun da ya gabata inda ya samu kashi 24.1% wanda ya kasance na farko a zaben da kuma ya ba shi damar zuwa zagaye na biyu na zaben shugaban kasar na ranar bakwai ga watan Mayu 2017.
A zaben shugabancin kasar zagaye na biyu Emannulle Macron mai sassaucin ra'ayi da fafata da yar takara mai tsananin ra'ayin rikau Marine Le Pen ta jami'iiyar Fron National.
Sakamakon wannan zaben kuma ya ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben da kashi 66.6%, a yayin da abokiyar hamayarsa ta FNm Madame le Pen ta samu kusan kashi 33.94% na yawan kuri'un da aka kada.
A yanzu dai Mista Macron ya kasance shugaban kasar Faransa mafi karancin shekaru da aka taba samu, tun bayan Louis-Napoléon mai shekaru 40 a 1848,
Haka zalika Macron shi ne na farko da aka taba zaba, ba daga manyan jam'iyyun kasar biyu ba, wato socialiste cewa da yan gurguzu da kuma 'yan ''Les Républicains''
Sabon zababben shugaban kasar ta faransa Emanuelle Macron, na da jan aiki a gabansa, musamman ma kan batun rashin aiki wanda ya nuna kasar kuta a cikin tsarayenta na turai, sai kuma batun tsaro wanda ya zo daidai da lokacin da kasar ke karkashin dokar ta baki saboda barazanar ta'addanci, ga kuma batun daya shafi maido da martabar kungiyar tarrayya turai bayan ficewar Biritaniya daga cikinta.
Wani babban kalubalen kuma shi ne na zaben 'yan majalisar dokoki da aka shirya gudanarwa a cikin watan Yuni.
A ranar Lahadi mai zuwa ne ake sa ran Mr Macron zai karbi ragamar mulki daga hannun shugaba Francois Hollande, wanda ya kasance shi kuma wani shugaban kasar faransa mafi yankwan jini ga al'ummar kasar, wanda kuma ya yi wa'adin mulki guda.
A shekarar 2007 ne, Macron ya auri malamarsa da ta koyar da shi a babbar makaranta, Brigitte Trognuex kuma ta ba shi tazarar shekaru 25, saidai har ba suda 'ya 'ya.