Amurka : Trump Ya Kori Shugaban Hukumar FBI
Shugaban Amurka Donald Trump ya kori shugaban hukumar binciken manyan laifukan kasar FBI James Comey, wanda tuni hakan ya haifar da kace-nace a kasar.
A cikin sanarwar Mista Trump ya ce FBI na daya daga cikin manyan hukumomin dake da martaba a idon Amurkawa, don haka sama mata da sabon shugabanci a yau zai bude mata wani sabon babi.
Hukumar FBI dai ita ce ke gudanar da bincike kan ko an samu wata alaka tsakanin tawagar yakin neman zaben Donald Trump da kuma kasar Rasha.
Gwamnatin Donalt Trump dai ta zargi Mista James Comey da yin sakaci da lamuran binciken imel din 'yar takara Hillary Cliton ta hanyar wallafawa manema labarai abubuwa dayawa.
Jam'iyyar demokrate dai ta kira matakin da babban kuskure wanda ta ce ya nuna karara yadda gwamnatin Trump ke da shakku akan binciken da ake kan rawar da Rasha ta taka a cikin harkokin zaben shugabancin kasar wanda sabilin hakan ne Cliton ta sha kaye.