Rasha Na Zawarcin Amurka Don Shawo Kan Rikicin Syria
https://parstoday.ir/ha/news/world-i20238-rasha_na_zawarcin_amurka_don_shawo_kan_rikicin_syria
A wani lokaci a wannan Laraba ce ake sa ran ministan harkokin wajen Rasha Sergio Lavrov zai kai ziyarci birnin Washington domin tattaunawa da mahukuntan Amurka kan batun rikicin kasar Syria.
(last modified 2018-08-22T07:00:05+00:00 )
May 10, 2017 01:19 UTC
  • Rasha Na Zawarcin Amurka Don Shawo Kan Rikicin Syria

A wani lokaci a wannan Laraba ce ake sa ran ministan harkokin wajen Rasha Sergio Lavrov zai kai ziyarci birnin Washington domin tattaunawa da mahukuntan Amurka kan batun rikicin kasar Syria.

Rasha dai na neman hadin kan Amurka kan wani shiri da take dashi na kawo karshen rikicin da yaki ci yaki cinyewa a kasar Syria.

Wannan ita ce ganawa ta farko da za'ayi tsakanin wani babban jami'in jami'in kasar Rasha da sabuwar gwamnatin Donald Trump na Amurka.

A yayin ziyara ta sa Mista Lavrov zai gana da shugaban kasar ta Amurka Donald Trump a fadar White, kafin daga bisani ya kuma gana da takwaransa na Amurkar Rex Tillerson.

Saidai ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da ake cikin zazzafar muhawara a Amurkar bayan korar shugaban FBI dake bincike kan zargin alaka da wasu makusantan Trump suka yi da Rasha a lokacin yakin neman zaben shugabancin Amurka na 2016.