Bukatar Rasha Na Hadin Kan Kasashen Duniya Wajen Yakar Ayyukan Ta'addanci
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi kira ga kasashen duniya da su hada kai don yakar ayyukan ta'addanci a duniya, ya kuma bayyana cewa kasar Rasha a shirye take ta yi aiki da dukkan kasashen da suke da wannan manufar.
Shugaban Putin ya bayyana haka ne a jiya Talata, a wani jawabin da ya gabatar a bukin "ranar nasara" wanda aka gudanar a birnin Mosco.
Ranar 9 ga watan Mayu na kowace shekara ita ce ranar nasarar da gwamnatin tarayyar Soviet ta lokacin da kawayenta suka samu a kan sojojin Nazi na kasar Jamus a karshen yakin duniya na biyu. A rannan ne sojojin Tarayyar Soviet suka kama birnin Balin Babban birnin kasar Jamus.
Bukin ranar nasara ta wannan shekarar dai ta zo a dai dai likacin da kasar Rasha take fafatawa da yan ta'adda a kasashen gabas ta tskiya da dama, da kuma a cikin gida.
Shugaba Putin ya kara da cewa dolene kasashen duniya su hada kai don yakar ayyukan ta'addanci, tsatsauran ra'ayin addini da kuma abinda ya kira ra'ayin Nazi bayan faduwar Jamus, wado Nio-Nazizim.
A halin nyanzu dai muna iya cewa ayyukan ta'addanci sun watsu kuma suna kara watsuwa a kasashen duniya, duk da cewa akwai kasashen duniya da dama suke bayyana anniyarsu da yakar wannan annoban.
Kasar Rasha a nata banagren ta dade yana yakar ayyukan ta'addanci a yankin kafaqas da kuma cikin gida. Sannan harin kunan bakin waken da aka kai a birnin Sinpitas Boog na kasar ta Rasha a cikin yan kwanakin da suka gabata ya dada jawo hankalin shuwagabannin kasar Rasha musamman shugaban Putin don ganin bayan ayyukan ta'addanci, tsatsauran ra'ayin addini da kuma ra'ayin Nazi bayan faduwar Jamus a karshen yakin duniya na biyu.
Wani abu mai muhimmanci wanda yakamata a lura da shi a nan shi, dole ne kasashen duniya su yaki ayyukan ta'addancin daga asalinsa wato daga tunani da ra'ayin da suke haifar da wadan nan ayyuka, amma yakar yan ta'adda ba tare da yin wani shiri na ganin bayan akidarsu ba zai kawo karshensu ba, kuma duniya ba zata taba rabuawa da ayyukan ta'addanci ba.
Sanin kowa ne kasashen yamma tare da wasu kawayensu na kasashen Larabawa suna goyon bayan kungiyoyin yan ta'adda a wasu kasashen larawa wadanda suka hada da Iraqi da Syria don cimma wasu manufofinsu ta hakan. Kasashen Saudia da Qatar a cikin kasashen Larabawa sune a gaba gaba wajen tallafawa kungiyoyun yan ta'adda ta Daesh da Jabhatun Nusra a kasashen Syria daIraqi.
Manufar wadan nan kasashe ita ke rarraba wadan na kasashe don bawa HKI damar cin karenta ba babbaka a yankin. Don haka , matukar ana samun wasu kasashe suna goyon bayan wasu kungiyoyin yan ta'adda a duniya to kuwa da wuya a ga bayansa nan kusa.
Sai kuma batun ra'ayin Nazi da yake kara karfi a wasu kasashen Turai, wadanda kuma suke tsananin adawa da yan gudun hijira daga wasu kasashen duniya zuwa tarayyar Turai, shi ma wani barazana ne musamman ga wadan nan kasashe masu daukar bakonninsun yan gudun hijira.