Amurka : Trump Ya Ja Kunnan Tsohon Shugaban FBI Kan Fallasa Bayanai
https://parstoday.ir/ha/news/world-i20322-amurka_trump_ya_ja_kunnan_tsohon_shugaban_fbi_kan_fallasa_bayanai
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ja kunnan tsohon shugaban hukumar binciken miyagun laifuka ta kasar FBI da ya kora wato James Comey kada ya yi wani bayyani ga manema labarai .
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
May 12, 2017 13:39 UTC
  • Amurka : Trump Ya Ja Kunnan Tsohon Shugaban FBI Kan Fallasa Bayanai

Shugaba Donald Trump na Amurka ya ja kunnan tsohon shugaban hukumar binciken miyagun laifuka ta kasar FBI da ya kora wato James Comey kada ya yi wani bayyani ga manema labarai .

Trump ya wallafa a shafinsa na twitter cewa  ya kamata Mista Comey ya tabbata cewa babu wasu nadadun bayyanansa kafin ya yi duk wani bayyani ga manema labarai.

Bayanai daga kasar dai sun ce abubuwa sun rincabewa shugaba Trump, musamen kan yadda ake ta kace nace kan batun korar Mista Comey daga shugabancin hukumar ta FBI, a daidai lokacin al'ummar kasar da duniya ke dakon binciken da ake kan ko Rasha tayi kutse a cikin harkokin zaben shugabancin kasar da ya gabata.

Shugaba Donald Trump dai ya bayyana a wata tattaunawa da tashar NBC cewa ya samu ganwa har sau biyu da wayar tarho da kuma cin abunci da Mista Comey wanda a yayinsa ya tambaye shi kan ko binciken FBI kan alaka da Rasha kafin zaben ya shafe shi ko kuma A'a, aman kuma Mista Comey ya mishi A'a.

A yanzu haka dai ana gudanar da bincike biyu a majalisar dokokin Amurka kan ko Rasha ta taka rawa a zaben da ake ganin shi ya yi sanadin faduwar yar takarar demokrate  Hillary Cliton a gaban abokin hammayarta Donald Trump na Rapablican na 2016.