Shugaban Kasar Faransa Ya Sanar Da Sabin Manbobin Gwamnatinsa
https://parstoday.ir/ha/news/world-i20464-shugaban_kasar_faransa_ya_sanar_da_sabin_manbobin_gwamnatinsa
Babban Saktaren Fadar Elysee ya sanar da sunayen manbobin sabuwar Gwamnatin kasar Faransa
(last modified 2018-08-22T07:00:07+00:00 )
May 17, 2017 14:21 UTC
  • Shugaban Kasar Faransa Ya Sanar Da Sabin Manbobin Gwamnatinsa

Babban Saktaren Fadar Elysee ya sanar da sunayen manbobin sabuwar Gwamnatin kasar Faransa

Tashar Telbijin din France 24 ta nakalto Alexis Kohler babban saktaren Gwamnatin kasar Faransa a wannan Laraba na cewa bisa yarjejjeniyar Shugaban kasar Emmanuel Macron da Sabon Firaministan kasar Edward Philip za mu bayyana sunayen sabin Ministocin kasar inda ya bayyana su daya bayan daya, sabuwar Gwamnatin dai na dauke da Maza 11 da kuma Mata 11 da suka hada da Ministoci 15 da kuma Mashawartar Ministoci guda 7.

Wadanda suka fi daukan hankalin al'umma a cikin sabuwar Gwamnatin ta Faransa sun hada da fitaccen dan gurguzun nan Jean-Yves Le Drian a matsayin wanda zai jagoranci harkokin kasashen waje da 'yar majalisa daga Kungiyar Tarayyar Turai Sylie Goulard a matsayin ministar tsaro.

Wasu manyan jami'ai da aka nada sun hadar da magajin garin birnin Lyon Gerard Collomb a matsayin ministan harkokin cikin gida sai mai matsakaicin ra'ayi Francois Bayrou da zai kula da harkokin shari'a, da mai ra'ayin rikau Bruno Le Maire da aka bayyana a matsayin ministan tattalin arziki.