An Kara Yawan Kame Kamen Yan Gudun Hijira A Kasar Amurka
Hukumar kula da yan gudun hijira a kasar Amurka ta bayyana cewa an kara yawan kame kamen yan gudun hijira a kasar a cikin watannu ukku na fadko na shugaba Donal Trump.
Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya nakalto hukuma mai kula da yan gudun hijira ta kasar ta na cewa yawan yan gudun hijiran da aka kama a cikin kwanani 100 na farko na shugabancin Donal Trump ya karu da kashi 37%, inda adadin kame kamen da aka yi ya kai mutane 41,318.
Labarin ya kara da cewa an kama yan gudun hijiran ne aka kuma tsare su dai dai lokacinda masu kula da lamura suka tabbatar da cewa kashi 3-4% ne kadai daga cikinsu aka taba kamawa da laifi.
Siyasar shugaba Donal Trump na gina katanga tsakanin Amurka da Mexico da kuma na hana musulmi daga kasashe 7 na duniya shiga kasar ta Amurka dai ya sha suka a cikin gida na wajen kasar.