Amurka : Trump Zai Yi Aiki Da Yarjejeniyar Nukiliyar Iran
Amurka ta ce zata yi aiki da yarjejeniyar nukiliyar da mayan kasashen duniya suka cimma da Iran karkashin gwamnatin tsohon shugaba Barack Obama.
Wata sanarwa da ma'aikatar diflomatsiyar Amurkar ta fitar, ta ce shugaba Trump zai mutunta yarjejeniyar data tanadi sasautawa Iran takunkumin tattalin arzikin da kakaba mata kamar yadda yarjejeniyar ta 14 ga Watan Yuli 2015 ta tanada.
Idan ana tune a lokacin yakin neman zabensa shugaba Donald Trump na Amurka ya yi alkawarin yayage yarjejeniyar da mayan kasashen da suka hada da Amurkar, Rasha, China, Faransa, Biritaniya da Jamus suka cimma.
Saidai ma'aikatar kudi ta Amurkar ta ce takunkumin data kakabawa wasu bangarori na Iran din na nan daram musamen kan masu ruwa da tsaki kan shirinta makamai masu linzami.
Wannan sanarwar ta Amurka na zuwa ne a yayin da ya rage kwana a kada kuri'a a babban zaben shugabancin kasar ta Iran a gobe Juma'a wanda shugaba mai barin gado Hassan Rohani madugun cimma yarjejeniyar ke sake takara.