Koriya Ta Kudu : Park Geun-hye Ta Gurfana gaban Kotu
(last modified Tue, 23 May 2017 11:18:05 GMT )
May 23, 2017 11:18 UTC
  • Koriya Ta Kudu : Park Geun-hye Ta Gurfana gaban Kotu

Tsohuwar shugabar Koriya ta Kudu Park Geun-hye ta musanta laifukan da ake tuhumarta da da aikatawa a yayin da ta gurfana gaban kotun birnin Seoul a yau Talata.

Ana dai zargin Uwargida Park da aikata ba daidai ba da kuma wasu laifuka da suka hada da cin hanci da rashawa da tozarta karfin mulki da kuma fallasa sirrikan kasa.

A karon farko kenan da tsohuwar shugabar ke bayyani a bainal jama’a tun bayan cafke ta a cikin watan Maris da ya gabata.

Koriya ta Kudu na da damar yanke hukuncin rai-da-rai ga duk wanda aka samu da  laifin cin hanci da karbar rashawa.