Kungiyar NATO Za Ta Shiga Kawancen Yaki Da IS
May 25, 2017 11:16 UTC
Kungiyar tsaro ta NATO ta ce za ta shiga kawancen kasa da kasa na yaki da kungiyar 'yan ta'adda ta IS, aman ba zata shiga yaki ba kai tsaye.
Irin wannan matakin da Amurka dake jagorancin kawancen dake yaki da kungiyar ta IS ta jima tana zawarci, tamakar babban sako ne na nuna hadin kan da ake da shi a yaki da kungiyar, kamar yadda sakatare janar na kungiyar ta NATO, Jens Stoltenberg ya shaidawa manema labarai a birnin Brusels.
Hakan dai na zuwa ne a yayin da ya rage yan sa'o'i kafin babban taron kungiyar ta NATO na yau Alhamis wanda shugaba Donald Trump na Amurka zai halarta a karon farko.
Tags