Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ya Taya Musulmi Murnan Shigowar Ramadan
(last modified Sun, 28 May 2017 05:17:18 GMT )
May 28, 2017 05:17 UTC
  • Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ya Taya Musulmi Murnan Shigowar Ramadan

Babban sakataren majalisar dinkin duniya António Guterres ya taya al-ummar musulmi a duk inda suke a duniya murnar shigowar wata mai alfama na Ramadan

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto António Guterres yana fadar haka ne a jiya Asabar bayan an bada sanarwan shigowar watan a mafi yawan kasashen musulmi. 

Babban sakataren yayi al-kawari kan cewa a cikin watan zai ziyarci daya daga cikin kasashen musulmi don nuna farincikinsa tare da su kan shigowar watan na azumi kuma ya dandani abinda suke samu a cikin watan. 

A nan kasar Iran da kuma mafi  yawan kasashen musulmi a jiya asabar ne aka fara azumin watan Ramadan inda musulmi zai kauracewa wasu abubuwa wadanda suka hada da shi da shi , daga safe har zuwa faduwar rana ko magarima na tsawon watan guda.