IS Ta Dauki Alhakin Kai Harin Philippines
kungiyar 'yan ta'adda ta IS ta dauki alhakin kai harin da ya yi sanadin mutuwar mutane 37 a wani gidan caca a birnin Manille na kasar Philippines.
A wata sanarwa data fitar ka kafar yada farfagandarta ta Amaq, kungitar ta ce wasu mayakanta ne suka kai harin, duk da cewa mahukuntan Philippines din sun nace kan cewa harin bana ta'addanci ne ba.
A cikin daren jiya ne wani dan bindiga ya kusa kai cikin gidan cacar tare da kona gidan, kafin daga bisani shi ma ya hallaka kansa a wani dakin Otel
Gidan cacar dai dake birnin Manille ya kone kurmus sakamakon harin da dan bindigar ya kai.
Tunda farko dai yan sanda a birnin sun ce mutane 36 ne suka hallaka a harin sakamakon shakkar hayaki na gobara data tashi a ginin.
Akwai dai ‘yan asalin kasashen ketare da dama da suka hallaka a wannan hari, wanda kuma a yayinsa wasu mutane kimanin 50 suka jikkta.