Dumamar Yanayi : Kamata Ya Yi A Tattauna, Ba Surutu Ba - Putin
https://parstoday.ir/ha/news/world-i20960-dumamar_yanayi_kamata_ya_yi_a_tattauna_ba_surutu_ba_putin
Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce ba zai yi jayaya da matakin da takwaransa na Amurka Donald Trump ya dauka ba na yin watsi da yarjejeniyar canjin yanayi ta Paris.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jun 02, 2017 13:51 UTC
  • Dumamar Yanayi : Kamata  Ya Yi A Tattauna, Ba Surutu Ba - Putin

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce ba zai yi jayaya da matakin da takwaransa na Amurka Donald Trump ya dauka ba na yin watsi da yarjejeniyar canjin yanayi ta Paris.

Putin ya ce yanzu abin da ya dace shi ne kawai a samar da mafita kan wannan batu ta yadda za' a tafi tare a tsira tare, amma ba a dinga yin surutu ba alhali shi Trump din ya ce zai amince a sake tattaunawa domin amincewa da wata yarjejeniyar.

Putin ya fadi hakan ne a yayin da yake jawabi a taron tattalin arziki a birnin Saint-Petersbourg inda  ya yi kira ga kasashen duniya su yi aiki tare da Trump kan sauyin yanayi.

Duniya dai na ci gaba da yin Allah wadai da matakin da Trump ya dauka na janye kasarsa daga yarjejeniyar rage dumamar yanayi da aka cimma a wata Disamban 2015 a birnin Paris.

Kasar Amurka ce dai ta biyu a kasashen da ke fitar da gurbataccen iska da ke dumama yanayi, aman Trump ya ce ya dauki matakin ne saboda irin illolin da yarjejeniyar za ta haifar wa tattalin arzikin kasarsa.